Ministar Kudi ta Nigeria ta bayyana a gaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa.
Da take amsa tambayoyi daga ‘yan kwamitin, ministar kemi Adeosun ta fada cewa ya zuwa yanzu kashi goma sha biyar ne kacal daga cikin 100 aka yi anfani da shi daga cikin kasafin kudin wannan shekarar da ta kusa karewa.
A cewar Minista Adeosun, watanni hudu ke nan da aka fara aiki da kasafin kudin, wanda ne Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya rattabawa hannu a watan shidda, yayinda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jinya a Ingila.
Sai dai kuma Dcanmajalisar Dattawa, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba na jihar Sokoto ya nemi babban bankin kasar da ma’aikatar kudi su bayyanawa kasa inda kudade sama da Naira biliyan dari shida suka shiga tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.
To amma shi kam Sanata Danjuma Goje, shugaban kwamitin kuddin na majalisar, yace ya gamsu da bayanan da ministar ta bayar.
Ga Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum