A yunkurin ganin an habaka wasanni a Najeriya, Ministan Matasa da wasanni na tarayyar Najeriya Mr. Sunday Dare, yace zai maida hankalinsa wajen gyara filayen wasanni.
Sunday Dare, ya bayyana haka ne a wata ziyarar da ya kai filin wasa na tunawa da Obafemi Awolowo dake Ibadan Jihar Oyo.
Inda ya nuna rashin jin dadinsa ganin yadda filin wasa mai dimbin tarihi ya lalalace, babu wasu kaya wasanni na zamani da aka tanada a filin.
Sabon Ministan, ya bayyana cewar hakan ya farune sanadiyar sakaci daga shuwagabanni da suka gabata.
Dare, wanda ya ziyarci wasu wuraren wasanni a kasar, domin gani da ido ya kara da ce wa, ma'aikatarsa zata bada himma wajen gyara dukkannin filayen wasanni, cikinsu akwai filin wasa na tunawa da Sir Ahmadu Bello, dake Kaduna; sai filin wasa na Moshood Abiola Abuja, filin wasa na Obafemi Awolowo da ke Ibadan kana da na birnin Lagas.
Dare ya ce akwai shirye-shirye kan wannan gyaran, kuma farkon abunda ma'aikatarsa zata fara aiwatarwa shine wannan batun.
Al'umman Najeriya da dama na san barka da jin irin wannan bayanan, da Ministan wasanni Sunday Dare yayi domin kawo gyara a harkar wasanni.
Facebook Forum