BIRNI N'KONNI, NIJER - Ministan kiwon lafiya na jamhuriyar Nijer Docteur Idi Illiyasu Mai Nassara, ya kai ziyara wasu cibiyoyin ajiyar magungunan yaki da zazzabin cizon sauro da ma asibitoci a kasar ranar Alhamis, domin tabbatar da cewa ana ba jama’a maganin cutar kyauta a duk fadin kasar.
Da yake magana da manema labarai, Mainasara ya ce ya kai ziyarar ne don ganewa idonsa yadda ake aikin yaki da zazzabin cizon sauro a asibitoci. Ya kara da cewa gwamnati ta dauki alkawarin bada maganin cutar kyauta ga yara da manya, don haka jama'a su lura.
Ruwan sama da ake ci gaba da yi kamar da bakin kwarya a fadin jamhuriyar Nijer ya janyo karuwar mutanen da ke kamuwa da cutar ta cizon sauro. Sai dai jama’a a wasu yankunan kasar kamar Birni N'Konni na cewa har yanzu ba su gani a kasa ba.
Don tabbatar da cewa ana ba manya da yara maganin kyauta a birane da kauyukan kasar, to dole ne gwamnati ta sa ma'aikatanta su sa ido kan aikin da kuma tsawatawa, don kar ya zamanto rijiya na bada ruwa guga tana janyewa.