Minista Nanono wanda ya fara aiki ba da dadewa ba, na wannan bayanin ne a wani taron hukumar bunkasa ingantaccen iri ta Najeriya da aka yi.
Ministan ya nuna damuwa akan cewa akwai hukumomin bincike da masana kan lamuran noma amma labari kawai a ke yi ba a samar da iri mai inganci da zai kai harkokin noma gaba kamar yadda Indiya ta yi nasarar zama mai nomawa da fitar da alkama kasashen ketare.
Haka kuma, Nanono ya nuna damuwa akan yadda ba a maida hankali akan wani itace mai albarka wato iccen gawo wanda bayan samar da taki, ya kan taimaka wajen yaki da hamada.
Ministan ya kuma ce a Nijar ko kai dan gidan Firai minista ne ba ka isa ka sare iccen gawo ba, amma ga shi nan ‘yan Nijar su na shigowa Najeriya su na kada iccen.
Bayanan ministan da alamu sun tsumar da mambobin hukumar kula da irin don su na ganin Najeriya na kan gaba da kasashen da ministan ya ambata a bangaren samar da iri mai inganci.
Daya daga cikin mambobin kula da hukumar, Ibrahim Musa, ya ce in a na maganar Najeriya wajen iri ko noma ba za a dauko missalin wata kasar makwabta ba.
Gabanin Najeriya ta gano fetur, kasar na dogara ne akan noma da kiwo amma yanzu ba a ma ga maciji tsakanin manoma da makiyaya.
Facebook Forum