Mutane da dama sun tsaya a cikin dogayen layukka dake wajen rumfunan zabe a birnin Bujumbura da kasar baki daya domin kada kuri’un su.
Wa'adin mulkin shugaban kasar a yanzu na shekaru biyar-biyar ne amma kwaskwarimar da ake son yi wa kundin tsarin mulkin zata baiwa shugaban karin shekaru bakawi akan karagar mulki. Kudin Tsarin mulkin kasar ya baiwa kowanne shugaba wa’adin mulki 2 ne kawai, amma ana ta ganin cewa sauya dokar zai baiwa Nkrunziza damar ya sake tsayawa zabe har sau biyu nan gaba.
Shi dai shugaba Nkurunziza wanda tun shekarar 2005 yake kan karagar mulki, an sake zaben shi a karo na uku a shekarar 2015, abinda ya saba wa dokar da ta tanadi yin mulki sau biyu kawai. Wannan matakin yana cikin yarjejeniyar da aka rattaba wa hanu don maido da zaman lafiya a shekarar 2000 wanda ya kawo karshen mummunar yakin basasa da aka yi a lokacin, wanda akalla mutane 1,200 suka rasa rayyukan yayinda wasu mutanen Burundi fiyeda 400,000 suka yi gudun jijira daga kasar.
Facebook Forum