Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea kuma jagoran tawagar 'yan wasan Super Eagles ta Najeriya Mikel Obi ya bayyana ajiye takalmansa daga buga wa Najeriya wasa.
Tun da farko dai dan wasan ya shaida wa 'yan jaridu cewa da zarar an kammala gasar cin Kofin nahiyar Afirka ta 2019, ita ce gasar karshe da
zai halarta wa kasarsa Najeriya.
Dan wasan mai shekara 32 da haihuwa ya buga wa Najeriya wasa 89, a tsawon shekaru 15, da suka wuce tun daga shekarar 2005, zuwa 2019, ya jefa kwallaye shida kacal.
Mikel yace yanzu lokaci yayi da ya kamata ya ba matasa dama domin su bada irin tasu gudumawa wa, musamman wadanda suka taimaka kasar ta lashe kyautar tagulla a gasar kasashen Afirka na bana.
Baban abun farin ciki da tarihi shi neMikel yace a kasar Masar ya fara harkar kwallo wa Najeriya a wani wasa kuma sai gashi ya ajeyi takalman sa a kasar ta Masar 2019.
Ya kuma buga wa Najeriya wasa a shekara 2003, a kungiyar 'yan kasa da shekara 17, yana mika godiyar sa ga jagorori da 'an wasa da magoya bayan Super Eagles.
Bisa damar da suka bashi ya haskaka a idon duniya da kuma wasanni masu kayatarwa da ya buga a matakin kasa-da-kasa daban daban.
Nasarorin da Mikel Obi ya samu a Super Eagles sun hada da lashe kofin kasashen Afirka a shekarar 2013, kuma yana cikin tawagar Super Eagles da ta zo ta uku a gasar na shekarun 2006, da kuma 2010.
Bayan haka yana cikin tawagar 'yan wasan da suka kai Najeriya wasan karshe a gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekara 20, inda ya kasance dan wasa mafi kwazo na biyu bayan Lionel Messi na Argentina da yazo na daya.
Facebook Forum