Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Me Shugabannin ECOWAS Za Su Je Yi Mali a Wannan Karon?


Wasu shugabannin yammacin Afirka
Wasu shugabannin yammacin Afirka

Wasu shugabannin yammacin Afirka, ciki har da tsohon shugaban kasar Najeriya za su je kasar Mali wacce ke fama da rikicin siyasa.

A cewar wani rahoton kamfanin dillancin labarai na AFP, za su je Mali ne domin "samar da maslaha".

A ranar Talata ne sojojin Mali suka hambarar da tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita, tare da tsare shi da frai ministansa da kuma wasu jiga-jigan gwamnatinsa.

A yau Juma'a ma, wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ta samu ganin shugaban. Tun ranar da aka hambarar da shugaban dai ba wanda ya ji komai daga gare sa.

Duk da dai sojojin sun sake biyu daga cikin jiga-jigan gwamnatin nasa a yau Juma'a, shugabannin na ECOWAS sun jadadda cewa dimokradiyya suke so a mayar a kasar.

Lamarin juyin mulkin ya janyo zaman dar-dar a yammacin Afirka, inda mutane ke fargabar cewa kasar mai cike da rauni za ta iya rugujewa.

A ranar Talata, kafin a hambarar da shugaba Keita, tsohon shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya gana da shugaba Buhari kan rikicin na Mali.

Tuni dai kungiyar ta ECOWAS ta dakatar da Mali daga kungiyar, ta kuma rufe iyakokinta a matsayin martani kan abubuwan da ke faruwa a kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG