Hukumomi a matakai daban daban na yin anfani da ranar wajen fadakar da jama'a, musamman matasa game da illar shan kwayoyi masu sanya maye.
Alhaji Abdullahi Abdul daya daga cikin kwamandojin hukumar hana sha da fatauci da sarafa miyagun kwayoyi ta Najeriya ko NDLEA a takaice, ya shaidawa Muryar Amurka mahimmancin wannan rana.
Yace ranar tana da mahimmanci garesu da kasa da kuma duniya gaba daya domin rana ce da majalisar dinkin duniya ta kebe a fadakar da al'umma illar shaye-shaye da safara muggan kwayoyi.
Alhaji Abdul yace da wuya a kayyade ko an samu raguwar masu anfani da muggan kwayoyi a Najeriya amma yace akwai masu shuka tabar wee-wee da dama a kasar. Yace hukumar NDLEA tana iyakar kokarinta ta gani cewa ta gano gonakan kuma ta konesu. Kullum suna gano gonakin tabar.
Duk da kokarin hukumar wajen fadakar da jama'a akwai alamar cewa hada-hadar shan kwayar na cigaba a tsakanin matasa. Malam Shehu Labaran wani magidanci a Minna jihar Neja ya bayyana fargabansu a matsayinsu na mahaifi. Yace akwai wani yaron abokinsu wanda tunda ya shiga harakar shan kwaya ya fita hankalinsa. Wasu matasan an daukesu zuwa asibiti saboda illar da shan kwaya ta yi masu. Wasu kuma suna nan suna yawo kan tituna saboda babu masu kaisu asibiti.
Malam Labaran ya shawarci hukumar NDLEA ta tashi tsaye ta hada karfi da karfe wajen yakar shan muggan kwayoyi da yanzu na nakasa mutane musamman matasa.
Ko baya ga tabar weewee da kokein dai da dama daga cikin matasan na yin anfani da wasu magunguna kamar su totalin da tiramol har ma da shakar kwata domin bugar da hankalinsu wanda a lokuta da dama sukan dangantashi da talauci ko kuma tsananin damuwa.
Kungiyoyi da dama na ganin akwai bukatar kungiyoyin addinai su tashi tsaye domin fadakar da jama'a illar sha ko yin anfani da duk wani abu mai batar da hankalin dan Adam.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.