Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru-Majalisar Dinkin Duniya Tayi Allah Wadai da kisan Masu Zanga-Zanga.


Daruruwan matasa ne suka yi zanga zanga ayankin Ingilishin sarauniyar Ingila a kamaru, ranar Lahadi data gabata.
Daruruwan matasa ne suka yi zanga zanga ayankin Ingilishin sarauniyar Ingila a kamaru, ranar Lahadi data gabata.

Ofishin kula da hakkin Bil'Adama na Majalisar ne yayi wannan furuci daga Geneva.

MDD tayi Allah wadai da kisan masu zanga zanga da ake zargin jami'an tsaro kamaru suka yi kan masu zanga zanga a yankin kasar na masu magana da harshen turancin Sarauniyar Ingila, a garuruwa da suke arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar kasar.

Ofishin kula da hakkin Bil'Adama na MDD yace wannan lamari ya auku ne ranar Lahadi daya ga watan nan. Daga nan ofishin yayi kira da a gudanar da bincike ba tareda nuna son zuciya ba danagne da lamarin.

kamar yadda rahoton da wakiliyar MA Lisa Schlein ta aiko daga Geneva ya fada , adadin wadanda suka halaka sakamakon matakin na jami'an tsaron kasar shine mutum 10.Amma wasu bahasin sunce mutane fiyeda haka ne aka kashe.

Kakakin hukumar kula da 'yancin Bil'Adama ta MDD Rupert Colville yace wasu majiyoyi masu tushe sun nuna cewa jami'an tsaro sun yi amfani da karfi da ya wuce misali.

Kashe kashen na ranar Lahadi data gabata ya auku ne sakamakon zanga-zanga a duk fadin yankin kasar na masu magana d a harshen turancin Ingila, wanda ya kai ayyana 'yancin gashin kan yankin wanda bashi da tasiri.

Ofishin kula da 'yancin dan'adam yayi kira da akai zuciya nesa, kuma yayi maraba da furucin shugaban kasar kamaru Paul Biya,wanda yayi Allah wadai da duk wani nau'i na tarzoma, daga nan yyi kira da a gudanar da shawarwari a zaman hanyar warware wannan rikici.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG