Wata mota shake da bama-bamai ta tarwatse a gidan gwamnati a Mogadishu babban birnin kasar Somalia, inda mutane dama su ka mutu.
Shugaban sashen motocin daukar majinyata na Mogadishu, Ali Muse, y ace fashewar ta yau Talata ta hallaka mutane sama da 60 ta kuma raunata wasu fiye da 40.
Shaidun gani da ido sun gaya wa Sashen Somaliyanci na Muryar Amurka cewa wasu ‘yan kunar bakin wake su biyu ne su ka tuka motar zuwa gidan gwamnatin, wanda ke dauke da ma’aikatu 8 na gwamnatin Somalia.
Kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida ta yi ikirarin kai harin.
Wani dan jaridar Somaliya da ke wurin, ya gaya wa Muryar Amurka cewa akasarin wadanda abin ya rutsa da su dalibai ne, wadanda su ka je Ma’aikatar Ilimi don binciko sakamakon jarabawar zuwa karatu a kasar Turkiyya.
Gwamnatin Somalia ta yi Allah wadai da wannan harin, ta ce harin ya nuna cewa har yanzu hadarin da ake fuskanta daga ‘yan ta’adda bai gushe ba.
Al-Shabab ta janye mayakanta daga birnin Mogadishu a cikin watan Agusta, ta amman ta cigaba da rike sassa da daman a kudanci da tsakiyar kasar ta Somalia. Kungiyar na gwagwarmayar nemar hambarar da gwamnatin wuccin gadin da ba ta da karfi, a wani yinkuri na kafa tsattsauran nau’in shari’ar Musulunci.