A jiya Litini ne wata kotu a kasar Maroko (Morocco) ta yanke ma wani matashin mawaki hukuncin zuwa kurkuku na tsawon shekara daya, saboda laifin rubutun batanci ga jami’an ‘yansanda a shafinsa na sada zumuntar yanar gizo. Mohammed Mounir, wanda ake wa lakabi da ‘Gnawi,’ shahararren mawakin zamani ne, wanda ya shahara a kasar.
Lauya mai kare matashin dan shekaru 31, ya ce ba wai laifin zagin da ya yi a shafinsa na Instagram ne ya sa aka yanke masa wannan hukuncin ba, matashin ya rubuta tare da raira wata waka da ta ke bayyana irin mawuyacin hali da jama’a ke ciki a kasar ta Maroko, inda ya ke bayyana rashin aikin yi a tsakanin matasa, da cin hanci da rashawa da ya yi katutu a tsakanin jami’an gwamnati.
Wakar tashi ta samu karbuwa inda mutane sama da miliyan 15 a fadin duniya su ka kalli wakar a shafin YouTube tun bayan wallafa ta a watan da ya gabata.
Cikin wakar tashi ya bayyana rashin adalcin mahukunta, da kausasan kalamai ga sarkin kasar, da kafafen yada labarai, inda su ka bayyana hakan da cin zarafin masarautar. Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa-da-kasa Amnesty International ta yi Allah wadai da hukuncin kotun.
Kotun, wadda ke birnin Sale, kusa da Rabat babban birnin kasar, ta yanke ma matashin hukuncin zama gidan kasu na shekara daya da kuma tarar dirham dubu daya. “Ni mawaki ne, kuma aiki na shi ne na kare kaina da kuma jama’ata, wannan ba shi ne karon farko da ‘yansanda ke cin zarafi na ba,” abin da Gnawi ya shaida wa kotun kenan.
Ya kara da cewa, “Tun da aka haife ni ake cin zarafi na. A harabar kotun kuwa, ‘yan uwa da masoyan matashin ne ke ta raira wakokin “Rayuwa mai karko gareka namu.”
Facebook Forum