Rundunar ‘yan sandan kasa da kasa(INTERPOL)ta fidda wata sanarwar gargadi dake yin kiran da kada a jinkirta kamo tsohon babban jami’in ayyukan leken asiri a zamanin Gwamnatin Moammar Gadhafin Libya, wanda yanzu haka ke hannun jami’an tsaron kasar Mauritania domin ya fuskanci shari’a a kotun kasa da kasa.
Sanarwar gargadin da rundunar ‘Yansanda ta kasa da kasa ta bayar jiya lahadi na karfafa cewa kada ayi sake da kamun da aka yiwa Abdullah al-Senoussi, da yake hukumomin Libya yanzu sun aike da bukatar a kamoshin.
Rundunar ‘yan sandan kasa ta kasa na zargin tsohon jami’in ayyukan leken asirin na Libya da laifin barnatar da kudaden al’ummar Libya ba tare da izni ba tare da yin amfani da karfin hukuma wajen takura ‘yancin Bil Adama don kawai cimma bukatarsa ta kansa.
Faransa aada kotun kasa da kasa dake shari’ar masu aikata laifukan yaki sun bukaci da a gurafanar da al-Senoussi gaban shari’a domin amsa laifukan cin mutumci da wulakanta Bil Adama.
Ana kyautata cewar al-Senoussi ya gudu daga Libya ne a lokacin da yaga zanga-zangar kin jinin Gwamnatin Gadhafi tayi tsanani. Hukumomin kasar Mauritania suka ce suna tsare da al-Senoussi tun daga ran Asabar da kamashi bayan saukarsa daga jirgin saman fasinjan Casablanca dauke da Fasfon Jabu na kasar Mali.