Tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Mauricio Pochettino, yace kofa a bude take ga duk kulob din da ke bukatar sa a nahiyar Turai.
Kocin mai shekaru 47 da haihuwa, wanda Tottenham ta sallame shi daga aiki a watan da ya gabata, bayan ya shafe shekaru biyar a kungiyar, wanda ta maye gurbin sa da Jose Mourinho.
"Kungiyoyi da dama na sha'awar yin aiki da shi" a cewar Pochettino."
Amman yace yanzu yana da bukatar ya tsaya gefe guda, domin ya kwantar da hankalinsa dan ganin abun da zai kasance.
Ana kuma alakantashi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, ko Arsenal wadda ita ma ta sallami nata kocin.
Pochettino, yace ya yanke shawarar cigaba da aikin horas da 'yan wasan, amma na farko shine zai dawo kasarsa ta Argentina, domin haduwa da dangi da abokai a kallah na kwanaki 10. Kafin daga bisani ya yanke shawarar kan makomarsa.
Facebook Forum