Wannan al'amari ne babba dake hana cigaban kasarsu da yankinsu.
Makon da ya wuce Algeriya ta tasa keyar mutane dari tara da goma sha bakwai, sai kuma a wannan satin ta sake dawo da mutane dari tara da arba'in da biyar da suka hada da yara dari ukku dacasa'in ukku da suka fito daga karn Kante.
Alatu Musgaskiya shugaban gundumar Alit yayi karin haske. Yace yawancin yaran iyayensu ne ke tafiya dasu, yayinda wasu kuma haya ake bada su. Amma da zara sun isa Algeriya sai a sasu bara ko kuma karuwanci.
Sabili da wannan danyen aiki da wasu halaye da ake sa yaran su yi ya sa ana cin zarafin yaran, musamman yara mata. Kamata yayi su tsaya kasarsu ta Nijar su yi karatu, walau na addinin Islama ko boko. Yace babu batancin da ya fi a bar yaro ya taso da yin bara ko lalata.
To saidai gwamnati da masu hannu da shuni na kokarin ganin an dakile wannan muguwar dabi'a.
Daraktan kyautata rayuwar mata a jihar Damagaran tace gwamnati ta kuduri daukan duk matakan da suka dace domin kawo karshen zuwa Algeriya yin bara ko kuma safarar yara.
Ga rahoton Tabari da karin bayani.