Wannan lamari ya sa wasu matasan kasar Nijar sun koma gida domin su rungumi noma maimakon gararamba da su ke yi a can Libya tare da rashin sanin tabbas inda suka dosa.
Rashin gwamnatin tarayya a kasar Libya da tabarbarewar tsaro inda sau tari bakin haure sukan rasa rayukansu, ya yi sanadiyar matasan Nijar masu cirani a Libya komawa kasarsu da zummar rungumar ayyukan gona.
Malam Muhammad Seni daya daga cikin matasan Nijar da suka baro kasar ta Libya yana mai cewa yanayinsu ya canza a Libya.
Ya ce da can suna samun biyan bukata amma yanzu ko ci da sha da kyar suke samu.
Baicin tabarbarewar tsaro, darajar kudin Libya ta fadi kasa warwas lamarin da ya sa 'yan cirani suna yin ayyuka ba tare da gani a kasa ba.
Dalili ke nan da ya sa matasan Nijar dake zuwa Libya ci rani barin kasarsu su koma gida.
A cewar Magajin garin Tinta Baraden sun kawowa matasan taimako sossai kuma tun da suna sha'awar yin noma sun basu tallafi.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.
.
Facebook Forum