Wata Maryam Laushi ta wata kungiyar matasa da wasu ma sun shiga majalisar wakilai inda suka mika bukatunsu.
Ita Maryam ta zanta da Muryar Amurka inda ta bayyana dalilin da suka sa suke neman a rage shekarun tsayawa takarar shiga majalisar wakilai daga talatin zuwa ishirn da biyar haka ma a rage ta majalisar dattawa daga talatin da biyar zuwa talatin.
Tace yanzu matasa sun kawo karfi a kasar suna kuma aiki tukuru. Da yawa cikin wadanda suke gwamnati yanzu masu taimaka masu da rubuta masu jawabansu yawancinsu matasa ne. Tace lokacin zaben 2015 matasa aka fi yin anfani dasu har aka kai inda ake yau. Saboda haka yakamata a hada kai da matasa, a basu zarafi domin su ma su yi aikin gwamnati ta fuskar rike mukaman siyasa.
Dangane da cewa aikin kirkiro dokoki ya na bukatar masu shekaru da dan dama abun da ya sa aka yi tsarin yanzu, sai tace haka ba ne matasa ma suna iya yin aikin. Tace idan matashi har za'a bar matashi dan shekaru goma sha takwas ya shiga soja ya rike bindiga kana in ya kai ishirin da daya yana iya kafa kamfani babu abun da zai hanashi zama majalisa ya kirkiro dokoki.
Akan yadda kudurin da suka gabatar har ya samu karatu na daya da na biyu yanzu yana kan na uku a majalisar wakilai sai Maryam tace tana ganin su ma 'yan majalisa sun gani cewa lokaci ya canza kuma gaba daya a duniya yanzu ana sa matasa cikin harkokin mulki.
A kan furucin da Musa Yola ya yi na cewa yakamata matasa su hakura da wuraren da suke su bar na gaba dasu su rike harkokin mulki sai Maryam tace ai kashi saba'in na al'ummar kasar matasa ne saboda haka yamata ana yi dasu, amma ba wai suna son su cire na gaba dasu ba ne gaba daya. Tace lallai suna bukatar iliminsu da shekarun da suka yi suna aiki su hada da nasu domin a yi aiki.
Dangane da wai hanzarin son tara abun duniya ga matasa ka iya kaisu shiga cin hanci da rashawa a lokacin da kasar ke yaki da wannan muguwar dabi'a saboda haka su dakata har sai manyan kasar sun gama yakin, sai Maryam tace akwai 'yan shekaru sittin ko fiye ma da har yanzu basu bar aikata halayaen banza ba. A ganinta ba shekarun mutum ba ne zasu hanashi aikata aikin asha amma hankali, da kwarewa, da kwatabta adalci su ne zasu sa ya iya aiki yadda ya kamata.
Ta yaba da kokarin Shugaba Buhari kuma tana zaton nan da shekaru uku abubuwa zasu gyaru.
Ga karin bayani.