Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasa Sun Yi Asarar Sana'a


Wasu matasa 'yan banga a Maiduguri
Wasu matasa 'yan banga a Maiduguri

Cigaba da rufe hanyar sadarwa a jihar Borno ya jawo ma dubban matasa asarar ayyuka da samun kudin shiga na more rayuwar yau da kullum.

Jihar Borno na daya daga cikin jihohi uku na arewa maso gabashin Najeriya da aka kakabawa dokar ta baci kimanin watanni biyar da suka wuce sanadiyar tashe tashen hankali da kungiyar Boko Haram take haddasawa a fafitikar da take yi domin kafa irin nasu mulkin addinin Musulunci.

Kimanin matasa dubu goma sha biyar dake sana'ar sayar da katin salula ko gyaran wayar tafi da gidanka suka samu kansu cikin halin lahaula wala kawati sanadiyar rufe wayar salula ranar 16 ga watan Mayu na wannan shekarar a jihohi uku da aka kakabawa dokar ta baci wadda jihar Borno na ciki. Lamarin ya sa wasu matasa da dama sun bar jihar yayin da wasun su kuma suka zama 'yan bangar siyasa. Wasu kuma suna yawo kwararo kwararo tamkar 'yan Allah Ya baku mu samu.

Halin da suka samu kansu a ciki ya sa wasu matasan sun kira taron manema labarai a babbar kasuwar tasu dake bakin gidan waya ko fasa ofi dake tsakiyar birnin Maiduguri. Kasuwar tana nan a rarake sabanin yadda take da kafin rufe hanyar sadarwar. Malam Ado Sani Mohammed Babao daya daga cikin masu sana'ar ya bayyana irin halin da suke ciki. Ya ce yawancinsu cin yau da kyar gobe ma da kyar. Bayan haka kuma ga lallurar yara. Wasu an korosu daga makaranta domin iyayen sun kasa biyan kudin makaranta. Ya ce sun yi kokarin jumrewa har sai a dawo da hanyar sadarwar amma abun ya cutura. Wasu sun sayar da kadarorinsu domin su samu abun ci.

Wani Malam Aliyu Yanta ya ce lokacin da akwai hanyar sadarwa sukan shiga kasuwa ba tare da ko sisin kwabo ba amma mutum ba zai koma gida hannu banza ba. Mafi yawan matasan masu iyalai ne. A halin da suke ciki yanzu sukan dan taimaka ma juna domin a rayu tare. Wasunsu da suka koma kekenapep idan sun zagayo sukan dan taimaka.

Malam Mustapha Isa ya kira gwamnatin Borno ta yiwa Allah da Annabi ta taimakawa 'yan waya domin halin da suke ciki. Ya ce wasu 'yan waya an koresu daga gidajen da suke haya.


Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00
Shiga Kai Tsaye



LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”
XS
SM
MD
LG