Shamsudeen Suleiman Inuwa, jami'in kungiyar dake daidata al'umma da gwamnati wato "Nigerian Intervention Movement", ya ce a zabe mai zuwa akwai kyakkyawar fahimtar cewa matasa ba zasu ta da zaune tsaye ba, sakamakon fadakarwa daga malamai da shugabannin.
Ya kuma ce a zaben da ya gabata yawaitar fadakarwar da malamai da shugabannin suka yi ne ya tabbatar da zaman lafiya, inda hakan ya zama kamar shaidar dake nuna cewa batutuwan zaman lafiya na shiga kan matasa.
Kwamared Shamsudden ya kara da cewa matasa sun farga da cewa sai da zaman lafiya ne ake samun ci gaba, domin kuwa suna da yakinin cewa da zarar sun yi bangar siyasa, 'yan siyasae na barin su a hannun hukuma ba tare da sun yo belinsu ba.
Ya kara da yin kira da hukumomin da suke da alhakin gudanar da zabe da jami’an tsaro da su jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya a zaben da za a yi ranar asabar a wasu jihohin, sannan ya ja hankalin matasa da su yarda da kaddara da zarar an bayyana sakamakon wanda ya lashe zabe.
Haka kuma Shamsudden ya kara jan hankalin al’umma akan su ma su yarda da dukkan kaddarar da ta zo wa jihar Kano.
Kan batun rashin damawa da matasa, ya ce kasashen Afrika basu waye da cewar matasa su ke da kyakkyawan kudorori da zasu kawo ci gaba ga kasar ba, don haka ne suke kin ba matasa damar da zasu yi amfani da kwakwalwarsu domin tabbatar da ci gaba.
Ga karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum