Darektan cibiyar yaki da cutar kanjamau na Majalisar Dinkin Duniya Micheal Sidibe ya bayyana cewa, kimanin matasa dubu dari bakwai ne suke dauke da kwayar cutar kanjamau a Najeriya.
Darektan ya bayyana haka ne a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Bisa ga cewarshi, kimanin daya cikin biyar na wadanda ke dauke da cutar kanjamau a Najeriya matasa ne tsakanin shekara 15 zuwa 32.
Ya kuma bayyana cewa, kashi 24% na matasan ne kawai suka san matakan da ya kamata su dauka na kare kansu daga daukar cutar, da kuma yada ta. Mr Sidibe ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta hanzarta kafa dokar hana nunawa masu fama da cutar wariya.
Bisa ga cewarshi, wadanda ke dauke da cutar, sun yi wahala sakamakon wariya da ake nuna mana fiye da cutar da suke dauke da ita.