Kotun da ta zauna a Kontagora a jihar Nejan ta yankewa matasan biyu hukuncin daurin shekaru bakwai da tarar kudi nera dubu saba'ain.
Matasan sun yiwa yarinya mai suna Aisha Rabiu fyade bayan da suka bata kwayoyin bugarwa a garin Kontagoran. Alkalin kotun Tanko Waziri ya yanke hukuncin daurin shekaru biyar ga Ahmad Zakari tare da tarar nera dubu hamsin a matsayin wanda kotun ta samu da laifin fyaden. Shi kuma Rufa'i Ahmad ya samu hukuncin daurin shekaru biyu tare da biyan tarar nera dubu ashirin a matsayin wanda ya taimaka aka tafka mugun laifin.
Barrister A.M. Sarkin Daji shi ne lauyan kungiyar lauyoyi mata dake kare yarinyar da aka yiwa fyade. Yace kotu tayi anfani da hujjoji da dama kafin ta yanke hukuncin. Yace na farko ya san mutane ba irin hukuncin da suka so ba ke nan. Amma duk yadda aka so abun, ita shari'a tana da hanyoyi daban daban na warware matsala. Kotu tayi la'akari da shekarunsu. Ta kuma yi la'akari da cewa basu taba aikata wani laifi ba. Hukuncin babu zabi domin ya zama kashedi ga wadanda watakila zasu so su yi irin hakan nan gaba.
Amma a nashi gefen mahaifin Aisha Malam Muhammed Rabiu yace hukuncin ya zo mashi da bazata. Yana zaton hukuncin zai fi haka to amma hakinsu duka suna kan mahukunta.
Su yara matasan sun ce sun gamsu da hukuncin da aka yanke masu, inji lauyansu Shehu Muhammed Kagara. Yace alkalin da ya yanke hukunci ya bi tsarin shari'a kuma yayi adalci. Sun bar wa Allah sauran lamarin.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.