A wajen taron wata kungiya dake da’awar kishin kabilu 372 na Najeriya an yi muhawara akan matakin da gwamnati ta dauka na ayyana ranar 12 ga watan Yuni ta zama ranar Dimokradiya a Najeriya.
Shugaban taron Muhammad Saidu Mai Dalailu ya ce ba daidai ba ne a dauki matakin na gwamnatin Najeriya a matsayin sadaukar da karramawar ga Abiola shi kadai ko kuma kabilar Yarbawa.
Mai Dalailu y ace zai yi wahala a sake yin irin abun da ya faru a zaben Abiola. Abiola Musulmi ne. Babagana wanda ya kasance mataimakinsa Musulmi ne. Ya ce gaba daya babu batun kabila ko addini aka fito aka zabesu.
Mai Dalailu ya ce idan ana gani hikima ce, me ya sa wasu basu yi ba can baya? Ko menene ma matakin ya yayyafa ruwan sanyi akan ciwon da wasu suke ji tun shekarar 1993, sun samu kwanciyar hankali.
Shi ko Barrister Surajo Usman Haske yana ganin an dauki matakin ne domin dacewar sa.
Amma Dan Audu na jam’iyyar adawa ta PDP ya ce bahaguwar dabara ce sauya ranar Dimokradiya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni saboda a cewarsa lokacin da lamarin ya faru babu irin kashe-kashe da kone kone da ba’a yi ba a Najeriya. Yana ganin an yi abun ne da wata manufa. A cewarsa gwamnatin Buhari ta gane akwai kurakurai saboda haka tana neman kuri’u ne shi ya sa take kame-kame.
Malam Isa Damagun yana ganin ya dace a bukaci hukumar zabe ta baiyana sakamakon zaben tukunna. Ya ce su basu gamsu da matakin ba. Basu ji dadinsa ba sam.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani
Facebook Forum