Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osibanjo ya kai ziyara sansanan ‘yan gudun hijira dake jihar Adamawa, daya daga cikin jihohin da aka girke sabuwar rundunar ‘yaki da kungiyar Boko Haram.
Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya tura shi yaje yaga halin da ‘yan gudun hijirar suke ciki. Yace gwamnatin tarayya zata hada hannu da gwamnatin jihar Adamawa wajen ganin ‘yan gudun hijirar sun bar sansanan ba da dadewa ba.
Daruruwan ‘yan gudun hijira ne suka tarbi mataimakin shugaban kasar, inda suka bayyana mashi bukatunsu. suka ce, abu na farko da suke bukata shine ganin sun koma gidajensu. Bisa ga cewarsu, kungiyar Boko Haram ta karkarya gadojin da suka hada kauyukansu, yayinda kuma aka kokkona mafiya yawan gidajensu.
Har wa yau, ‘yan gudun hijirar sun bukaci a tallafawa malaman sa kai da suka shafe watanni tara suna koyarwa a sansanin.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar Michika da Madagali, Adamu Kamal ya bayyana farincikin ganin gwamnatin tarayya ta kai ziyara yankin da kuma alkawarin biyan bukatun ‘yan gudun hijirar.
Ga cikakken rahoton da wakilin sashen hausa Ibrahim Abdul’aziz ya aiko.