Sama da iyalai dari shida ne masu karamin karfi wadanda galibinsu mata ne matan 'yan kungiyar majalisun ECOWAS suka tallafawa domin sauwake masu nauyin iyali da kuma kawo masu doki akan matsalolin da suka biyo bayan ambaliyan ruwa ko kuma suke cikin gudun hijira domin tashe-tashen hankula.
Taimakon ya hada da shinkafa da sukari da sabulun wanka da wanki domin ragewa jama'a radadin sayen kayan masarufi gaf da kama azumi.
Hauwa Ambali kakakin kungiyar matan majalisun dokokin ECOWAS tayi karin bayani. Tace su suka tattara kudi domin su tallafawa mata gajiyayyu na kasashe 15 dake cikin ECOWAS. Wasu kasashen ana yaki. Wasu kuma babu zaman lafiya. Sun fara da kasar Niger domin kasar Musulmai ce kuma ga azumi ya karato.
Taimakon ya samu karbuwa ga al'umma kuma sun bayyana jin dadinsu. Sun ce an taimaka masu domin dama can suna cikin rashi. Sun yi addu'a Allah Ya sa masu albarka.
Ga rahoton Abdullahi Ahmadu Mamman.