Daga cikin 'yan majalisar dattawa dari da tara mata takwas ne kacal. Haka ma idan an kafa sabuwar majalisar watan gobe adadin mata ba zai canza zani ba a maimakon sa ran da mata suka yi cewa zasu karu.
To amma a majalisar wakilai mata sun samu koma baya inda yawansu ya ragu ba kamar yadda aka yi tsammani ba. Da akwai mata ashirin da hudu amma yanzu sun ragu zuwa goma sha shida, wato sun ragu da takwas ke nan.
Wata da guguwar Buhari ta hanata dawowa majalisar wakilan Ka'amuna Ibrahim Kadi ta nuna rashin jin dadinta da lamarin.Tace sun ragu ba domin basu iya siyasa ba ne ko rashin yadda dasu. Tace a gaskiya ma mutane sun fi yadda dasu fiye da maza domin idan sun zo Abuja ba sa kulle ofisoshinsu kamar yadda maza suke yi.Tace to amma duk yadda aka yi siyasar Najeriya siyasar kudi ce. Tace su mata basu iya sata ba saboda haka basu da irin kudin da maza suke dashi.
Rashin kudin ya hanasu cin zabe. Idan aka cigaba da hakan an tambayeta ko za'a dama da mata a siyasar kasar. Tace bata da shakka za'a yi domin idan aka taka rawa aka ga bata yi ba dole su dawo su zabi mata.
Ga karin bayani daga Medina Dauda.