Amina ta ce abin da ya ja hankalinta ta fara sana'ar dinki, shine ita mace ce mai son kwalliya da gayu, don haka ne ta ce me zai hana ta maida hankali ga harkar dinki tunda ita mai son gayu ce.
Ta ce ta fara wannan sana’a ne bayan da ta kammala jami’a, sannan ta fara ne da dinkakkun kayayyaki, da mutane ke zuwa su saya. Ta ce tana bukatar mata da su maida hankali wajen sana’oin dogaro da kai, domin tun da ta fara aiki ta ce ta daina neman kudaden a wurin iyayenta.
Amina ta ce tun da ta fara wannan sana’ar, kasancewar ita yar jihar Borno ce, hakan yasa ta bude wuraren dogaro da kai ga matasa dake Borno, inda ta bude "Enterprenuers Hub" inda suka debi matasa, tare da koya musu sana’oin hannu.
Amina dai ta fara sana’ar hannu tun tana jami’a a ajin karshe, ko da yake a lokacin bata maida hankali sosai a matsayin sana'a ba, illa a matsayin nishadi. Amma sai ta fara samun kwastomomi daga cikin dalibai, da haka ne ta fara hada jarinta da riba, daga nan har ya kai ta da bude shago a yanzu.
A saurari cikakken rahoton daga wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir.
Facebook Forum