Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata 7 Da Ke Jerin Sunaye 28 Da Tinubu Ya Turawa Majalisa


Wasu Matan da za a ba Minista a Najeriya
Wasu Matan da za a ba Minista a Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yana kan hanyar kafa tarihi na ba mata mukaman Ministoci mafiya yawa a tarihin kasar.

Ranar Alhamis Shugaba Tinubu ya turawa Majalisar Dokokin Tarayyar kasar sunaye 28, da gwamnatin ta bayyana a matsayin rukunin farko na jerin sunayen wadanda ake shirin nadawa mukaman Ministoci.

Banda kafa tarihi na yawan matan da za a ba mukaman ministan, har wa yau, an kafa wani tarihin na samun mace mafi karancin shekaru a jerin matan da aka mika sunayensu.

Wasu Matan da za a ba Minista a Najeriya
Wasu Matan da za a ba Minista a Najeriya

Matan bakwai sun hada da Dr. Betta Edu, ‘yar shekaru 36, wacce ita ce mace mafi karancin shekaru da za ta zama Minista. Dr. Betta, ta kasance mace mafi karancin shekaru da ta taba rike mukamin shugabar reshen mata na jam’iyar APC mai mulki a watan Maris na shekarar bara. Banda haka kuma ta zama mafi karancin shekaru da aka zaba a matsayin mai ba Gwamnan jihar Cross Rivers Benedict Ayade shawara kan kula da lafiyar al’umma a shekara ta 2022, kafin a ba ta shugabancin kwamitin yaki da cutar Korona a shekara ta 2020. Dr, Betta ta yi aiki a matsayin kwamishinar lafiya ta jihar Cross Rivers kafin ta ajiye aikin a shekara ta 2022.

Akwai kuma Imaan –Suleiman Ibrahim daga jihar Nassarawa, wadda ta yi aiki a matsayin mai ba karamin Ministan Ilimi Chukwuemeka Nwajiuba, shawarwari kan harkokin sadarwa, a shekara ta 2019. Gwamnan jihar Nassarawa Injiniya Abdullahi Sule ya zabe ta a matsayin membar Majalisar tattalin arziki a jihar.Yanzu haka ita Kwamishinar Gwamnatin Tarayya ce a hukumar kula da ‘yan gudun hijira.

Dr. Betta Edu
Dr. Betta Edu

Sai Kennedy Ohaneye, wadda ‘yar kasuwa ce, kuma mace daya tilo da ta tsaya takarar shugaban kasa karkashin jam’iyar APC, kafin ta sauka ta barwa Tinubu a ranar zaben tsaida dan takarar jam’iyar. Akwai kuma Stella Okotete, wadda ita ma ‘yar siyasa ce, wadda ta rike mukamin shugabar reshen mata na kwamitin shirye- shiryen babban taron jam’iyar APC na kasa inda aka tsaida dan takarar shugaban kasar jam’iyar.

Sauran matan da ke cikin jerin sunayen Ministocin sun hada da Hannatu Musawa, wadda lauya ce kuma ‘yar gwaggwarmayar kare hakkokin mata, ‘yar fitaccen dan siyasar nan Musa Musawa daga jihar Katsina. Kafin sa sunanta a jerin sunayen Ministocin, a watan Yuni Shugaban kasa Bola Tinubu ya zabe ta a matsayin mai bashi shawarwari na musamman kan tattalin arziki da suka shafi al’adu da ayyukan shakatawa. Akwai kuma Dr. Doris Uzoka-Anite tsohuwar kwamishinar Kudi ta jihar Imo, wadda ta kuma tsohuwar manaja ce a bankin Zeneth.

Sai kuma tsohuwar ‘yar Majalisar Wakilai Nkeiruka Onyejeocha wadda a lokacin da take Majalisa tana daya daga cikin kusoshin Majalisar. Kungiyar ma’aikatan Majalisa ta bata lambar yabo lokacin da take Majalisar sabili da bisa ga cewar kungiyar, ta yi fice a matsayin ‘yar Majalisa mace da tafi hobbasa a Najeriya.

Hannatu Musawa
Hannatu Musawa

Mata a Najeriya suna kyautata zaton samun ci gaba a karkashin gwamnatin Tinubu a yunkurinsu na samun kaso 35% na mukaman siyasa da suka dade suna nema. Sai dai duk da yake an sami mata fiye da yadda aka yi a lolutan baya, idan aka yi la’akari da yawan matan da Shugaba Tinubu ya ba mukami I zuwa yanzu, za a iya cewa, har yanzu tsugune bata kare ba.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG