Masu zanga zagar a kasar Masar sun kutsa ofishin jakadancin Isira’ila a birnin Alkahira a jiya juma’a bayan da suka rushe katangar dake kewaye da ginin.
Wannan mataki yasa ala tilas jakadan Isira’ila a Masar, Yitzhak Levanon ya ranta zuwa filin saukar jiragen sama yau asabar da safe domin ya fice daga kasar.
Yau asabar aka ga Yizhak Levanon da iyalinsa da kuma wasu ma’aikatan ofishin jakadancin Isira’ila a filin saukar jiragen sama, suna jiran wani jirgin saman soja da zaiyi jigilarsu. Jami’an Masar sunce masu zanga zangar sun jefo daruruwan takardu daga cikin ginin.
A jiya juma’a masu zanga zangar suka yiwa ofishin jakadancin caa, suka rushe katangar dake kewaye da ginin. Su kuma jami’an tsaron Masar da suke wurin basu ce dasu kala ba, baletana kuma su dauki matakin hana masu zanga zangar kutsawa ofishin jakadancin.
Tun dai lokacinda aka hambarar da tsohon shugaban Masar Hosni Mubarak a watan Fabrairu aka samu karin kiraye kirayen cewa, Masar ta kawo karshen amfani da yarjejeniyar samun zaman lafiya ta tarihi data kula da Isira’ila a alif dari tara da saba’in da tara, kimamin shekaru talatin da biyu da suka shige.
A watan jiya fushin yan Masar ta karu, a lokacinda sojojin Isira’ila bisa kuskure suka kashe jami’an yan sandan Masar guda biyar a kusa da kan iyaka, a lokacinda su sojojin na Isira’ila suke maida martini ga harin da wasu yan yakin sa kai suka kaiwa Isira’ila.