Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Zanga-zanga a Mali Sun kara Fitowa


Masu zanga-zanga a Mali
Masu zanga-zanga a Mali

Daruruwan mutane sun sake gudanar da zanga-zanga a babban birnin Mali don nuna goyon bayansu ga gwamnatin sojan da ta yi juyin mulki a kasar, yayin da ake ci gaba da muhawara kan lokacin da kasar za ta koma wamulkin farar hula. 

Watannin da aka kwashe ana zanga-zanga akan rikicin ‘yan ta’adda, tashin hankalin kabilanci da cin hanci da rashawa a kasar ne suka zafafa har sojoji 'yan tawaye suka kama shugaban kasar, suka kuma yi mashi juyin mulki a ranar 18 ga watan Agusta.

Wata kungiya da ake kira June 5 Movement ce ta jagoranci zanga-zangar, kuma wata sabuwar kungiya da ke kiran kanta Popular Movement of September 4 ta shirya wani gangami da aka yi a Bamako jiya Talata.

Wasu masu zanga-zanga a Mali
Wasu masu zanga-zanga a Mali

Bayan juyin mulkin, kwamitin sojan da ke mulki a kasar yayi alkawarin shirya sabon zabe, da farko sojojin sun ce zasu jagoranci kasar a matsayin gwamnatin rikon kwarya tsawon shekaru uku, daga nan a koma wa gwamnatin dimokradiyya, kafin daga baya suka rage lokacin zuwa shekara 2.

“Muna son sojojin sun jagoranci kasar a matsayin gwamnatin riko har lokacin da zasu dauka, a cewar Hamza Sangare, wani mai shago a lokacin da aka yi zanga zangar Bamako.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG