Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Jaddada Muhimmancin Gwajin Jini Ga Masu Niyyar Aure Don Gujewa Samun Karin Masu Cutar Amosanin Jini


A bikin zagayowar ranar wayar da kai akan cutar amosanin jini a duniya, masana kiwon lafiya, da masu bada tallafi, da masu lalurar, na yi wa gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki tuni kan girman cuta tare da yin kira ga iyaye da su bada muhimmanci ga gwajin jinsin jini ga matasa masu niyyar aure.

ABUJA, NIGERIA -Taken wannan rana da aka ware don wayar da kan al’umma akan ciwon amosanin jini wato sikila na wannan shekarar shi ne “muhimmancin kula da kai ga masu dauke da wannan cuta.”

Ranar 19 ga watan Yuni na kowacce shekara ne kasashen duniya ke bikin ranar cutar sikila ta duniya, wadda da farko Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar a matsayin wani kuduri na yaki da cutar a shekarar 2008.

A yayin da ake ci gaba da aikin fadakarwa game da cutar, kwararrun likitoci a Najeriya na jaddada muhimmancin kula da kuma magance wannan cuta. Dr. Halima Bello Manga, kwararrar likita ce a fannin jini, ta ce fiye da rabin yaran da ake haifa da sikila a duniya a Najeriya ake haifarsu kuma ga shi babu kwararru da suka san kan cutar a kasar.

A Najeriya ana samun masu kamuwa cutar sikila kimanin 150,000 a duk shekara, a cewar Dr. Halima.

Shugabar gidauniyar Impact Sickle Cell, kuma uwa da ta kula da danta da ya yi fama da cutar sikila, Halima Nagado, ta ce ita da maigidanta jinsin jini mai dauke da sikila (AS) suke da shi, shi ya sa suka haifi da mai lalurar. Ta kara da jaddada muhimmancin yin gwajin jinsin jini kafin aure.

Duk da kokarin masana da ma hukumomin lafiya na wayar da kan al'umma, mutane da dama musamman a karkara, na yi wa gwajin jinsin jini kafin aure rikon sakainar kashi wanda ke maida hannun agogo baya wajen kawo karshen cutar sikila a Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf.

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Jadada Mahimmancin Gwajin Jini Ga Duk Masu Niyyar Aure Don Gujewa Karin Masu Fama Da Ciwon Sikila
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Tasirin Da Zaben Donald Trump Zai Yi A Harkokin Kasashen Duniya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:50 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG