An sami rahotannin cewa mayakan sakai masu cewa suna da’awar Islama suna rusa gine ginen wuraren tarihi da al’adun gargajiya a Timbuktu.
Shaidu sun gayawa Muriyar Amurka cewa mayakan sakai ‘yan kungiyar Ansar Dine dauke gatura da wasu makamai sun kai hare hare kan wuraren tarihi.
Haka kuma shaidun sun gayawa Muriyar Amurka cewa an rusa wani wurin tarihi na wani fitaccen malami da ake jin waliyi ne Sidi Mahmoud. Hukumar kimiyya da ilmi da al’adun gargajiya UNESCO ta saka Timbuktu cikin jerin wuraren da suke da dumbin tarihi, wadan da suke cikin hadiri ahalin yanzu.
Hukumar ta UNESCO tace Timbuktu ya kasance fadar masana da addini da cibiyar yada addinin Islama a duk fadin Afirka a karni na 15 da 16.
Hukumar UNESCO ta fada a shafin dandalin ta na internet ranar Alhamis cewa, ta tsaida shawarar saka Timbuktu cikin jerin wurare da suke cikin hadari sabo da fada da ake yi a yankin.