NIGER, NIGERIA - Wannan Matsala dai tasa tuni masu sana’ar buga burodi suka fara daukar matakin rufe kamfanoninsu na buga burodin a wasu yankuna na Nigeria.
Alhaji Lawali Muhammad shugaban kamfanin Shukura Bread a Jihar Neja, kuma mataimakin shugaban kungiyar masu buga buredi a yankin Arewacin Nigeria ya ce babbar matsalarsu ita ce tashin farashin fulawa da sukari na yin burodin.
Shi ma Malam Ibrahim Salisu, daraktan kamfanin Marhaba Bread, ya ce suna ci gaba da bai wa jama’a hakuri saboda yawan karin farashin burodin da ake samu a yanzu.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin talaka suka fara kokawa akan wannan matsala.
A yanzu dai hukumomin a Najeriya na dora alhakin tashin farashin kayan ga yakin da kasar Rasha ke gwabzawa da kasar Ukiraine, kamar yadda sakataren gwamnatin Jihar Neja Ahmed Ibrahim Matane ya shaida mana.
Sakamakon wannan matsala an fara ganin karancin buredi ko kuma tsadarsa, abinda da yake daya daga cikin cimaka mai sauki a tsakanin ‘yan Nigeria.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari: