Rahotanni a baya bayan nan daga Najeriya na cewa, mutanen da suka kamu da cutar coronavirus sun kai 288 yanzu, amma an sallami wasu 51 daga asibiti. Mutum 7 kuma sun rasa rayukansu sanadiyar cutar.
Sai dai a yayin da gwamnatin Najeriya ke neman dakile cutar coronavirus wasu na ganin kamar an manta da batun matsalar tsaro, hakazalika a wasu kasashen na duniya musamman batun tsaron dake da alaka da ‘yan ta’adda da sauran masu tada kayar baya kamar masu garkuwa da mutane a Najeriya.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da na shugabannin gargajiya a Najeriya na ganin idan an bugi jaki, sai a bugi taiki. Kuma idan an tuna da likitoci dake yaki da cutar coronavirus, to ya kamata a tuna da sojojin dake yaki da ‘yan ta’adda a kasar.
Basaraken gargajiya Oba Adekunle Oyelude Makama, na Kuta a jihar
Osun, ya nuna rashin jin dadinsa akan yadda wasu ‘yan kasar ke kushe ayyukan sojojin Najeriya a yaki da ‘yan boko haram, amma suna fifita sosjojin kasar Chadi.
A jiya ne dai gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari domin sanar da shi halin da ake ciki,
bayan harin da sojojin kasar Chadi suka kai wa ‘yan boko haram har cikin kasar Najeriya.
A saurari Karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum