Masu zanga zanga a Misra suna ci gaba da neman sojoji dake suke mulkin kasar suyi murabus nan take, kwana daya bayan da shugaban mulkin sojan kasar, Field Marshall Mohammed Hussein Tantawi, ya bada sanarwar daukan matakan sassauci domin rage adawar masu zanga zangar.
A yini na biyar masu zanga zanga suna cike a dandalin Tahrir, har an bada labarin an kara tsakanin masu zanga zanga da kuma jami’an tsaro. Ance an kashe akalla mutane 35 cikin kwanaki biyar a arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga zanga a birnin Alkahira, da kuma wasu birane.
Kwamishinar kula da hakkin Bil-Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay, tana kira ga hukumomin Misra su kawo karshen abinda ta kira “A zahiri, nuna fin karfi”. A sanarwa da ta bayar yau laraba, ta kira hotunan da suka nuna ana lakadawa masu zanga zanga dan Karen duka” duk da cewa an kama su, yana “matukar tada hankali”.
Jiya Talata, Tantawi wadda shine shugaban majilisar koli ta mulkin sojan kasar, yayi alkawarin hanzarta shirin mika mulki ga farar hula, da zaben shugaban kasa kamin karshen watan Yuli na badi.
Haka kuma Tantawi, ya bayyana sha’awar kaddamar da kuri’ar neman jin ra’ayin jama’a kan neman sojojin su mika mulki cikin hanzari.
Haka kuma ya bada sanarwar ya karbi murabus na majalisar ministocin kasar, karkashin jagorancin PM Essam Sharaf, amma zata ci gaba da aiki har sai an nada magada.
Amma dubun dubatan ‘yan Misra dake dandalin Tahrir sunki amincewa da wadan nan matakai cewa sun gaza.Suna son sojoji su mika mulki yanzu.
Ana sa ran fara zaben wakilan majalisar dokokin kasar ranar litinin, kuma Field Marshall Tantawi yayi alkawarin babu fashi. Duk da haka ‘yan hamayya suna bayyana shakkun za a yi zaben kamar yadda aka ayyana.