Wannan al'amarin na rashin biyan diyar tare da rashin cika alkawuran samarda ababen more rayuwa ga al'ummomin masarautar ya jefa yankin cikin wani yanayi mara dadi.
Mai martaba sarkin Suleija Malam Awal Ibrahim yace sun share dogon lokaci suna hakuri saboda haka lokaci yayi da ya kamata gwamnatin Najeriya ta dubesu da idon rahama. Yace sun yi hakuri, kuma hakuri baya baci. Zasu cigaba da hakuri Allah kuma ya taimakesu ,inji sarkin.
Dangane da abun da suke bukata sarkin yace arzikinsu dake cikin kasa a biyasu saboda an kwace filayen da arzikin dake cikinsu. An yi masu alkawura da yawa amma babu wanda aka cika lamarin da ya hana yankin Suleija cigaba. Yace idan Abuja suka yi rigimarsu su ne suke wahala. Yayi fatan Allah zai ba gwamnati zarafin warware maganar.
Shi ma dan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar yankin Suleija din Onarebul Abubakar Lado yace kudi kimanin nera biliyan talatin suke bukata a matsayin diya. Saboda haka ya taba tada maganar a zauren majalisar.
Kwamishanan labarai na jihar Neja Jonathan Batsa da yake magana akan lamarin yace 'yan Niger Delta suna neman su mallaki man kasarsu amma su an kwace kasarsu da albarkatun ciki gaba daya ba'a biyasu diya ba. Yace duk filin da aka sayar a Abuja ya kamata a basu wani abu ciki.
Yanzu gwamnatin jihar Neja ta kafa wani kwamiti a karkashin shugabancin Janar Idris Garba. Kwamitin zai dubi hakkokin da ya kamata a bayar kamar yadda gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ke cewa. Inji gwamnan akwai alkawura da aka yi da yawa da ba'a cika ba. Yace yanzu sun farga zasu kuma tsaya su tabbatar kowa ya samu hakkinshi.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.