Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Zatayi Gyaran Fuska Ga Yarjejeniyar Zaman Lafiya Da Isra'ila?


PM Turkiyya Racep Tayyib Erdogan yake jawabi ga kungiyar kasashen larabawa.
PM Turkiyya Racep Tayyib Erdogan yake jawabi ga kungiyar kasashen larabawa.

PM Masar Essam Sharaf yace yarjejeniyar zaman lafiya da kasar ta kulla da Isra’ila a 1979, ana iya yi masa kwaskwarima.

PM Masar Essam Sharaf yace yarjejeniyar zaman lafiya da kasar ta kulla da Isra’ila a 1979, ana iya yi masa kwaskwarima. PM ya bayyana haka ne a hira da yayi da tashar talabijin ta kasar Turkiyya, Alhamis.

Mr Sharaf yace yarjejeniyar da aka kulla a sansanin hutun shugaannin Amurka da ake kira Camp David, ana iya masa gyaran fuska ako da yaushe, muddin yin haka zai amfani yankin da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Shugabannin mulkin sojan kasar sun sha nanatawa cewa zasu mutunta dukkan yarjejeniyoyi da Masar ta kulla a baya da wasu kasashe ciki har da wacce ta kulla tsakaninta da Isra’ila.

Canza yarjejeniyar ba tareda amincewar Isra’ila da Amurka ba zai sa kasar ta daina samun tallafin na dubban miliyoyi daga Washington.

Zaman dar dar tsakanin Masar da Isra’ila yana kara tsanani tun bayan hambare shugaba Hosni Mubarak cikin watan Febwairu, ya sake dagulewa a hare hare kan iyakokin kasashen biyu.

Ahalin yanzu kuma, jiya Alhamis, yankin Falasdinu ya yi alwashin zai nemi cikakken amincewar majalisar dinkin duniya ta zama wakiliya mai cin gashin kai a majalisar. Yankin ya kuduri aniyar gabatarwa MDD wan nan bukata makon gobe duk da rashin amincewar Isra’ila da Amurka, duk da haka ta nuna alamar zata iya ci gaba da shawarwarin neman wanzar da zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG