Masar zata janye jakadanta daga kasar bani Isra’ila domin nuna bacin ran kashe wasu jami’an tsaronta da aka yi a lokacin da Isra’ila ta kai hare-haren ramuwar gayya kan ‘yan gwagwarmaya a bakin iyakar kasashen biyu.
A yau asabar majalisar zartaswar Masar ta ce zata janye jakadanta har sai ta ga sakamakon binciken da Isra’ila zata gabatar a kan wannan lamarin. Har ila yau, majalisar ta ce tana son shugabannin Isra’ila su nemi gafarar kalamun riga-malam-zuwa-masallaci da suka yi game da Masar.
Isra’ila ta bayyana damuwa game da tabarbarewar tsaro a zirin Sinina na Masar tun lokacin da shugaba Hosni Mubarak ya sauka a watan fabrairu. Rundunar sojojin bani Isra’ila ya ce ‘yan bindigar da suka kai hari a kudancin Isra’ila ranar alhamis, sun shiga ne daga Gaza ta hanyar Sinina, duk da matakan tsaron da Masar ta kara a yankin.
Masar ta ce an kashe mata dakarun tsaro biyar a lokacin da sojojin Isra’ila suka bi sawun ‘yan bindigar. Masar ta gabatar da takardar kuka a rubuce ga Isra’ila jiya jumma’a.
Har ila yau, majalisar zartaswar Masar ta bukaci jakadan Isra’ila dake al-Qahira da ya bayyana gabanta domin tattaunawa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Isra’ila yace jami’ai su na tattaunawa a kan wannan shawara ta Masar.
Wannan lamari yana kara tankiya tsakanin kasashen biyu da suka kulla yarjejeniyar zaman lafiya a 1979.