Hukumomi a Masar sun kama tsohon ministan cikin gida Habib el-Adley, da wasu takwarorinsa biyu,wadanda ake bincike kan zargin rashawa.
Banda minista el-Adley,hukumomin kasar jiya Alhamis sun kuma tsare ministan hukumar yawon bude ido,Zuhair Garana,tsohon ministan gidaje Ahmed el-Magrabi,da kuma Ahmed Ezz, fitaccen dan kasuwan karafa,wanda a da wakili ne a jami’yya shugaba Hosni Mubarak mai mulkin kasar.
Tshon ministan cikin gida Adley,wanda yake da iko kan rundunar jami’an tsaron kasar mai karfin jami’ai dubu dari biyar ne ake aza wa laifin mummunar farmaki da yansanda suka kai a farkon zanga zangar a ranar 25 ga watan Janairu wadda daga bisani ya tilastawa tsohon shugaba Mubarak a yin murabus ranar jumma’a data shige.
El-Adley ya yi shekaru 12 yana ministan harkokin cikin gida.
Dukkan mutanen hudu suna fuskantar zargin halatta kudaden haram,amfani da ikonsu ta hanyoyi da basu dace ba,da kuma satar dukiyar jama’a.