Hotunan Wasu Wasannin Damben Marigayi Muhammad Ali Tun Fara Dambensa
Hotunan Wasu Wasannin Damben Marigayi Muhammad Ali Tun Fara Dambensa

2
Zakaran damben ajin masu nauyi na duniya Muhammad Ali, tsaye a kan Sonny Liston, wanda ya buge cikin minti daya da fara dambensu a Lewiston dake Jihar Maine ranar 25 Mayu, 1965. Muhammad Ali shi kadai ne ya taba rike kambin damben duniya na ajin masu nauyi har sau uku.

3
Muhammad Ali yana kalubalantar Sonny Liston da ya tashi su ci gaba da bugawa, a bayan da shi Liston a lokacin ya ki yarda ya kira Ali da sabon sunansa, yana kiransa da tsohon sunansa Cassius Clay.

4
Muhammad Ali a lokacin da ya doke zakaran damben duniya na wancan lokaci, George Foreman ya kwace masa kambi a gwabzawarsu ta Kinshasa a tsohuwar kasar Zaire, ranar 30 Oktoba 1974. Wannan karawa ce aka yi mata lakabin "Rumble In The Jungle."

5
George Foreman lokacin da zai dunguri kasa a karawarsu da Muhammad Ali a Zaire