Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tabbatar da Ole Gunnar Solskjaer, a matsayin kocinta na dindindin.
Solskjaer, wanda tsohon dan wasan gaba ne a kungiyar, ya kasance a matsayin kocin rikon kwarya bayan da kungiyar ta sallami tsohon kocinta José Mourinho ranar 19 ga watan Disamban shekara 2018.
Ole ya jagorancin kungiyar a wasanni 19, inda ya samu nasara a wasannin 14, ya yi kunnen doki sau 2, an kuma doke shi a 3, shine kocin da yafi samun maki a dukkani gasar firimiya lig a wannan lokacin.
Kungiyar ta Manchester ta cimma yarjejeniyar kwantiragin shekaru uku tare da Ole Gunnar Solskjaer.
A yayin da yake dan wasa a Manchester Solskjaer, daga 1996 zuwa 2007 ya samu nasarar zurara kwallaye har guda 126 cikin wasanni 366, da ya buga.
A cikin jawabansa kocin ya ce a lokacin da yazo Manchester United ya dauketa tamkar gida ne a gareshi, Kasan tuwar ya buga mata wasa kuma gashi itace babbar kungiya kwallon kafa ta farko da ya fara koyarwa, don haka ya gode wa shuwagabaninta yan wasa ma'aikata da dukkan magoya bayan wannan kungiya bisa irin damar da aka bashi a Manchester.
Shima Mataimakin Shugaban kungiyar Ed Woodward, ya yaba wa kocin bisa irin na mijin kokarin da yayi a lokacin da ya zo kulob din a matsayin mai rikon kwarya kuma ya fidda ita cikin halin da ta shiga na koma baya.
Facebook Forum