Kungiyar Manchester City ta zama kungiya mafi daraja a gasar Firimiya, bisa kididdiga na Football Finance 2017/18, da aka fitar.
Manchester City ta kai darajar zunzurutun kudi har fam biliyan £2.364, daga ita sai Manchester United a matsayi na biyu da take da darajar fam biliyan £2.087, inda ta fado da fam miliyan 376.
Hakan na da alaka da irin albashi mai tsoka da kungiyar ke biya da kuma asarar da ta tafka.
Nazarin da aka yi a cibiyar kasuwanci ta jami'ar Liverpool, an gano cewa duka darajar gasar ta Firimiya lig yanzu ta kai fam biliyan £14.7 wato ya fadi
da kaso 1.6 cikin 100 a 2017/18.
Tottenham tana da darajar fam biliyan £1.83, sai Liverpool fam biliyan £1.615, Chelsea kuwa tana da darajar fam biliyan £1.615 ne, ita kuwa Arsenal ta yi baya zuwa fam biliyan £1.368 sakamakon rashin buga gasar zakarun Turai a bana, inda a shekara mai zuwa ma take fuskanatar barazanrar rashin buga gasar.
Facebook Forum