Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man City Ta Kafa Tarihin Lashe Gasar Premier League So Hudu A Jere

📸 AP * Wannan tsohon hoto ne na 'yan wasan kungiyar Man City yayin da suke murnar lashe gasar Premier League na bara
📸 AP * Wannan tsohon hoto ne na 'yan wasan kungiyar Man City yayin da suke murnar lashe gasar Premier League na bara

Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta lashe gasar Premier League na kasar Ingila bayan ta lallasa West Ham da ci 3-1 a wasan karshe na kakar bana a filin wasar Etihad na birnin Manchester.

Kungiyar kwallon kafar Manchester City ta lashe gasar Premier League na kasar Ingila bayan ta lallasa West Ham da ci 3-1 a wasan karshe na kakar bana a filin wasar Etihad na birnin Manchester.

Phil Foden, wadda ya lashe lambar yabon gwarzon dan wasar kakar bana ne ya zura kwalaye biyu a mintuna na biyu da na 18.

Sai dai jim kadan kafin ytafiya hutun rabin lokaci, Mohammed Kudus ya rama wa West Ham kwallo daya a minti na 42 da buga wasan.

Mintuna 14 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci City ta sake farkewa, wannan karon, Rodri ne ya kara zura wa City kwallo a dai dai minti na 59 da buga wasan.

Wannan shi ne karo na farko a tarihin gasar da wata kungiy za ta lashe gasar so hudu a jere.

Man City ta lashe gasar a kakar 2020/2021, 2021/2022, 2022/2023 da 2023/2024, inda a kakar 2022/2023 ta lashe gasar lig lig, FA Cup da gasar zakarun turai wato Champions League.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG