Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MALI: Amurka Ta Yi Tur da Hari Kan Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya


Wasu ojojin kiyaye zaman lafiya a filin saukar jiragen sama dak Bamako babban birnin kasar
Wasu ojojin kiyaye zaman lafiya a filin saukar jiragen sama dak Bamako babban birnin kasar

Amurka tayi Allah wadai da harin kwantan bauna da aka yiwa jerin gwanon motocin Sojojin kiyaye sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali, inda aka kasahe mutane shida da raunata wasu guda biyar.

Harin dai ya faru ne akan wata hanya mai tazarar kilomita 45 kudu maso yammacin birnin Timbuktu dake arewacin Mali. Kungiyar al-Qaida ce ta fito ta dauki alhakin harin.

A wani bayani da aka fitar a yammacin jiya Alhamis jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power, ta nuna jimamin ta ga iyalan mutane shidan da suka rasa rayukan su a dalilin harin, wanda baki ‘dayan su ‘yan kasar Burkina Faso ne.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ci alwashin cewa wannan harin bazai hana Majalisar Dinkin Duniya taimakawa ‘yan kasar Mali ba wajen aikin kawo zaman lafiya a kasar.

Wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun lura da cewa hare haren da ake kaiwa sojan kiyaye sulhu na iya zama laifukan yaki a karkashin dokar kasa da kasa.

XS
SM
MD
LG