A taron manema labarai da ya gudana a dakin taro na Tatari Ali Polytechnic dake Bauchi shugaban kungiyar malaman kwalajin Muhammad Bala Yakubu yace akwai abubuwa guda bakawi da suka tattauna a kai da hukumomin ilmi na jiha da na tarayya wadanda har yanzu ba’a cikasu ba.
Muhammad Bala Yakubu ya ba al’umma hakuri da wannan yajin aikin da suka fara yana cewa ba sonsu ba ne amma kuma ya zama wajibi domin mahukunta da abun ya shafa su zabura su yi abun da ya kamata.
Kafin su shiga yajin aikin wai sun bada wa’adi na kwana 21, da ya wuce suka kara kwana 10 amma gwamnati tayi kunnen lashi. Yace baicin rashin biyan su albashi na wata da watanni basu da kayan aiki a dakunan gwaje gwaje da bincike kana yawancin gine-ginesu suna neman rushewa saboda rashin kula dasu.
Kawo yanzu sun kusan shekara biyu suna fama da rage masu albashi. Misali, maimakon a biya mutum albashi cikakke sai a biyashi kashi sittin cikin dari kuma dole ya hakura. Makarantun mallakan jihohi ma wasu sun yi watanni 14 ba’a biyasu ko kwandala ba, inji Muhammad Bala Yakubu.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani
Facebook Forum