Kafin a tantance shi an yi sa-in-sa tsakanin ‘yan jam’iyar PDP da kuma na APC mai mulki wadanda ke da rinjaye a majalisar dattijai. Shugaban marasa rinjaye na jam’iyar PDP, tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio, shine ya tashi ya fara jawabi cewa, yaune aka mika rahoto da kwamitin da’a da tsawatarwa na majalisar dattatawa a kan shi tsohon gwamnan, saboda haka tunda ba a riga an ba ‘yan majalisar rahoton nan ba , basu karanta shi ba, basu yi muhawara a kai ba, su ‘yan PDP dake majalisar dattawa, ba zasu yiwa wannan tsohon gwamnan wata tambaya ba.
Wannan manuniya ce cewa, dama suna so ne su hana tantance tsohon gwamnan, su nemi a sake sa wata ranar ta tantance shi. Abinda suka so shine rahoton nan da kwamitin ya mika, a ba kowanne dan majalisar dattawa, ya karanta ya fahimce abinda rahoton ya kunsa, so koma majalisa suyi muhawara a kan rahoton kafin su san matakin da ya kamata su dauka a kan tsohon gwamnan kafin wani zaman tantancewa domin su san tambayoyin da ya kamata su yi masa.
Shi dai tsohon gwamnan dai ya taho da shirinsa, domin ya kawo rahoton da yace gwamnatin jihar Ribas ta rubuta a kan mulkinsa da kum ako an same shi da laifi ko kuwa babu. Yace a shirye yake y aba dukan ‘yan majalisar rahoton su karanta wanda a ciki babu inda akace an same shi da kowanne irin laifi na yin sama da fadi da dukiyar al’umma.
Ga cikakken bayanin Madina Dauda