Sama da wata guda ke nan da shugaban yake Ingila game da wata cuta wadda ba'a bayyana ko wacce iri ba ce ga jama'ar kasar.
Mr. Patrick Ekeli shi ne shugaban majalisar da akasarinsu 'yan kasa da shekaru 14 ne zuwa kasa, ya kuma ce kamata ya yi duk ilahirin 'yan Najeriya su tashi su yi wa shugaban addu'a.
Amma kuma hakan bai samu ba dalili ke nan da su yara suka yanke shawarar yi wa shugaban addu'a.
Yaran da suka taru a Minna babban birnin jihar Neja sun fito ne daga kowace jihar kasar Najeriya musamman domin gudanar da addu'a ma shugaba Buhari.
Abdulrazak Idris na cikin wadanda suka karanta addu'o'i wa shugaba Buhari bayan an kammala sallar Juma'a a babban masallacin Juma'a na Minna.
Shugaban majalisar limaman jihar Neja Shaikh Isa Fari ya ce gudanar da addu'a a wannan lokacin shi ne ya fi mahimmanci.
Baya ga addu'ar ta yau majalisar yaran ta ce za ta gudanar da addu'o'i ranar Lahadin nan a mijami'un Najeriya.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani.
Facebook Forum