Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Kolin Harkokin Shari’ar Musulunci Ta Najeriya Ta Kalubalanci Shekau


Majalisar kolin shari'a
Majalisar kolin shari'a

Majalissar kolin harkokin Shari'a a Najeriya ta mai da martini akan barazanar da shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi faifan bidiyon da ya fitar a baya-bayan nan.

A wani taron manema labarai da majalissar ta kira a Kaduna game da barazanar da Shekau ya yi a faifan bidiyon da ya fitar ta cewa lokaci ya yi da ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya farga.

Daya daga cikin manyan malaman addinin Musulunci a Najeriya, Sheik Abdulwahab Abdullahi Mohammad, ya kalubalanci Shugaban Kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau game da faifan bidiyon da ya fitar cewa har in ya cika jarumi, to ya fito yayi gaba-da-gaba da jami’an tsaro.

Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da batun matsalar tsaro a Najeriya yake dada jan hankalin 'yan kasa masamman ganin irin barazanar tsaron da aka fuskanta a kasar cikin wannan wata na Fabarairu.

Domin karin bayani, a saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

majalisar kolin shari'a
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:46 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG