Farfasa Ishak Oloyede na majalisar kolin yace rikicin 'yan shiya da sojojin abun bakin ciki ne kuma yana da tada hankali.
Majalisar kolin ta harkokin addinin Musulunci na kokarin aika wata tawaga mai karfi zuwa birnin Zaria domin binciko aininhin gaskiyan abun da ya faru. Ta kuma nemi bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.
Majalisar tana son a kafa wata hukumar bincike da zata yi aiki babu rufa-rufa cikin gaskiya da adalci domin gano gaskiyar abun da ya faru. Majalisar tace duk wanda aka samu da laifi lallai ya fuskanci hukunci.
Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina ya nemi jin ta bakin Malam Yakubu Yahaya wanda yanzu shi ne ya ke jan ragamar harkokin 'yan shiya a Najeriya. Akan yawan mutanen da suka rasu yace ana batun daruruwa ne domin idan basu kai dubu ba to kadan zasu kasa. Ko mata da aka kashe sun fi tamanin sai kuma maza wajen dari shida zuwa bakwai.
Inji Malam Yakubu Yahaya har yanzu jami'an tsaro sun kewaye wajejen kungiyar tare da gidan babban malaminsu.
A cewar Air Commander Ahmed Baba Gamawa mai murabus bai kamata mutane su dinga daukan doka a hannunsu ba. Bai kamata ana tare hanya ba koda ma talakawa ne balantana manyan jami'an tsaro. Yace 'yan shiya sun rike hafsan sojoji Janar Buratai har tsawon awa guda sun hanashi wucewa. Yana ta rokonsu su yi hakuri su bashi hanya amma suka ki.
Ga karin bayani.