Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Yi Sauraren Bahasi Akan Cutar Coronavirus


Sakataren Gwamnatin Tarrayya kuma Shugaban Kwamitin Ko ta Kwana wanda Shugaban Kasa ya nada, tare da Ministan Kiwon lafiya Osagie Ehanire da Shugaban Hukumar hana yaduwar cututtuka Chikwe Iheazu, sun gurfana a gaban Majalisar dokoki inda aka yi musu tambayoyi akan yaduwar cutar coranavirus da yadda za a iya dakile yaduwar ta.

Mayan 'yan kwamitin sun kwashe sa'o'i sama da hudu suna amsa tambayoyin daya bayan daya a zauren majalisar, inda suka yi bayanin irin shirye-shiryen da suke yi wajen hana yaduwar cutar da kuma dakile ta baki daya.

Onorabil Shehu Ahmed S. Fulani mai wakiltar Maru da Bungudu a Jihar Zamfara ya ce, a lokacin da ake yin irin wannan muhimmin abu na kiwon lafiya akan nemi bayanai domin a sanar da wadanda ake wakilta irin matakan da ake dauke na kare su, tunda duk wakilan sun fito ne daga wurare daban-daban da ake bukatar kariya daga cutar COVID-19.

Dan majalisa Magaji Aliyu Da'u ya ce, ba akan matakan kawai aka tsaya ba, an kai har ga tambayar irin kudaden da aka tara daga hanun manyan ‘yan kasuwa na cikin gida irin su Dangote da Abdulsamad Rabi'u da kuma wasu kudaden daga kasashen waje da aka ce an kai su Babban Bankin Najeriya an ajiye, da kuma ko ta wane hannu wadannan kudaden ke shiga, me ake yi da su, kuma da umurnin wa ake amfani dasu?

wadanan su ne abubuwa da Majalisa ta nemi sanin su kuma amma ba ta gamsu ba, majalisar ta yi alkawalin bin diddigi wadannan kudade.

Majalisar ta yanke shawarar zama kowace talata har sai an daga takunkumin hana yawo baki daya.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG