Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Najeriya Ta Sake Aikawa Da Dokar Zabe Da A Ka Yi Wa Gyaran Fuska Ga Shugaba Buhari


taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade
taron yan majalisa da sanatoci da aka yi a hade

A can baya shugaba Buhari ya ki rattaba hannun amincewa da sabuwar dokar zaben da majalisar dokoki ta gabatar masa, saboda a ganinsa, ta saba wa tsarin dimokaradiyya da ya ba da dama da zabin hanyoyin tsayar da 'yan takara.

Majalisar dokokin Najeriya ta sake tura dokar zabe da ta yi wa gyaran fuska ga shugaba Buhari don amincewa da sanya mata hannu zuwa doka.

In za'a iya tunawa, shugaba Buhari ya ki sanya hannu kan dokar tun da farko, don ta kunshi yin zaben ‘yar tinke na fidda ‘yan takara daga jam’iyyu, lamarin da shugaban ya ce sha'anin tsaro da kashe kudi ne suka sa hakan bashi da alfanu.

Kazalika shugaban ya ce in an bar dokar yanda ta ke za'a takaita damar jam’iyyu na fidda ‘yan takara ta zabi daban-daban irin na tsarin dimokaradiyya.

Majalisar dokokin dai ta bi bukatun shugaban sau da kafa kan cire sashen da shugaban ke ganin ba shi da fa’ida, inda a yanzu ta bude damar jam’iyyu kan iya amfani da zabi daban-daban, da suka hada da ta hanyar wakilai, ‘yar tinke ko ma daidaitawa wajen fidda dan takara.

Shugaban ya na da wata daya daga yanzu don sanya hannu kan kudurin zuwa doka.

XS
SM
MD
LG