Majalisar dai ta ce Binciken Wasu kudade ne har kimanin naira Miilyan 250 da kowane shugaban karamar Hukuma ya ciyo bashi daga Banki domin gudanar da ayyukan raya kasa ne yasa suka dauki matakin dakatar da Wadannan Shugabanni.
Shugaban kwamitin binciken yadda aka kashe wadannan kudade da majalisar ta kafa Hon. Malik Madaki Bosso ya ce Shugabannin kananan Hukumomin sun ki bari Majalisar ta binciki ‘yan kwangilar da suka bai wa ayyuka a yankunansu shi ya sa suka Dauki wannan mataki kamar yadda yayi Karin Bayani.
“Abunda ya kawo dakatar da wadannan ciyamomi guda goma sha biyar, da muke binkice. Bincike muke ba mu gama binciken ba, saboda suna saka mana hannu, idan ciyaman bai kan kujera, baya wurin, ba yadda za a yi ya ce kar ayi kaza, shi ya sa muka dakatar dasu don mu yi aikinmu mu gama.”
Mai tsawatarwa na bangaren marasa rinjaye a majalisar Hon. barista Bello Agwara ya ce wannan mataki da majalisar ta dauka baya da alaka da siyasa.
“Ba zancen siyasa a lamarin nan, idan aka ce ko wani abu zauren majalisa ya dauka mataki a kai aka fassara shi ta harkar siyasa ba za a yi aikin majalisa ba kenan. Ko da gobe ne majalisa za ta rufe, wa’adin aikinsu ya kare akwai aikin da ya kamata ta yi saboda a daidaita al’amura su yi kyau to dole ne za ta yi.”
To sai daya daga cikin shugabannin Kananan Hukumomin da Majalisar ta ce ta dakatar, Shugaban karamar Hukumar Rijau, Alhaji Bello Bako, ya ce ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa.
“Ba su da wannan hurumin, babu wata doka da ta ba su wannan ikon, saboda haka muna nan a matsayinmu na ciyamomi muna nan muna shirye-shirye ai mun saba shiga kotu da su. Za mu bi hakkin mu.”
A yanzu dai majalisar zata jira amincewar Gwamnan Jihar Alh. Abubakar Sani Bello akan wannan Mataki.
Saurari cikakken rahoton daga Mustafa Nasiru.